ylliX - Online Advertising Network DA DUMI DUMI Daliban Jami'ar Adamawa dake Mubi za su shafe watanni hudu a gida bayan watanni 8 - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

DA DUMI DUMI Daliban Jami’ar Adamawa dake Mubi za su shafe watanni hudu a gida bayan watanni 8

DA DUMI DUMI || Daliban Jami’ar Adamawa dake Mubi za su shafe watanni hudu a gida bayan watanni 8

Bayan shafe tsawon watanni takwas Jami’o’in Najeriya mallakin gwamnatin tarayya da kuma wasu wadanda suke mallakin jihohi, tsun duma yajin aiki wanda kungiyar malaman jami’oi ta kasa ASUU ke yi kafin ta janye yajin aikin a wannan satin.

Jami’ar Modibbo Adama wanda ke Yola da kuma jami’ar jihar Adamawa wanda ke garin Mubi sun fitar da sanarwa kan ranar da dalibai zasu koma azuzuwa domin cigaba da karatu kamar dai yadda sauran jami’o’i a kasar suka fitar da sanarwa.

Sai dai a wani bangaren da takardar sanarwar da jami’ar Jihar Adamawa dake Mubi, tafitar a yau wanda ke dauke da jadawalin yadda kakar zangon karatu na bana zai kasance wato (Academic Calendar) yabar baya da kura inda daliban da suke matakan azuzuwan karshe da kuma na kusa dana karshe (300L, 400L,500L) suka fara nuna rashin gansuwar su kan yadda aka tsara kalandar wanda zai tilastawa daliban wadanan azuzuwan zama na watanni har 4 agida bayan kammala jarabawar zangon kaka ta farko wanda zasu gama shi tun (December to April)

Yayin tattaunawar wakilin yola24 da wasu daliban sun bayyana takaicinsu kan yadda zasu koma gida suyi har wata 4 a zaune bayan wanan yajin aikin da suka shafe har watanni 8 sunayi

Sanan sunyi kira ga shuwagabanin jami ar da su gaggauta gyara kalandar domin kuwa su ayanzu karatu suke da bukata ba zaman gida ba

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button