LABARAI/NEWS

DA DUMI-DUMI: EFCC ta sake kama akanta janar da badakalar wasu Biliyan 90 bayan biliyan 80 na farko, yanzu kudin sun kama Biliyan 170

DA DUMI-DUMI: EFCC ta sake kama akanta janar da badakalar wasu Biliyan 90 bayan biliyan 80 na farko, yanzu kudin sun kama Biliyan 170

…ya ambaci sunan wani Ministan da manyan jami’an gwamnati a cikin badakalar

Daga Muryoyi

Bayanai sun nuna a yayin bincikarsa, Idris ya bayyana sunan wani minista tare da wasu manyan jami’an gwamnati da ke da hannu wurin damfarar N170 biliyan.

Jaridar The Nation tace kawo yanzu Idris yana bada hadin kai wurin binciken da ake masa inda a halin yanzu har an gayyaci wani sakataren gwamnatin tarayya da Idris ya ambata.

Majiya ta sanar da cewa, Idris ya sha alwashin mayar da wasu tsabar kudi zuwa lalitar gwamnati yayin da ya ke rokon EFCC da ta bada belinsa.

Me zaku ce?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button