LABARAI/NEWS

DA DUMI-DUMI: Jam’iyyar APC Ta Gama Zaban Wanda Zai Gaji Buhari A Zaben 2023 ~ Majiya

DA DUMI-DUMI: Jam’iyyar APC Ta Gama Zaban Wanda Zai Gaji Buhari A Zaben 2023 ~ Majiya

Wasu majiyoyi daga jam’iyyar APC na luguden-lebe cewa shugabancin jam’iyyar na yin wani yunkuri na kule-kulle ta kasa na ganin yankin da za ta ba tikitin takarar shugaban kasa a 2023.

Majiyar ta ce, tuni dai APC ta fara shirye-shiryen mika tikitinta ga yankin Arewa maso Gabas, lamarin da ka iya ruguza begen Tinubu na gaje Buhari.

Daya daga cikin majiyoyin da suka yi magana da jaridar This Day a ranar Talata, 17 ga watan Mayu, ta ce da gaske APC na duba yadda a karshe za ta tantance shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan a matsayin wanda zai tsaya takara a 2023.

Majiyar da ta nemi a sakaya sunanta ta ce: “Abin da majalisar kasa ke kokarin yi shi ne ta mara wa Lawan baya da dimbin wakilai da aka kafa na ’yan majalisa na baya da na yanzu wadanda gyaran zai ba su damar halartar irin wadannan tarurruka. “Suna cikin yanki mai kusan mutum 4,000, wanda da alama za su nuna goyon baya ga Lawan, don haka ne ma suke kokarin sake gyara dokar domin dacewa da son su da lissafinsu.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button