ylliX - Online Advertising Network DA DUMI DUMI Nuhu Ribadu ya nemi kotun Daukaka kara da ta baiwa jam'iyar APC damar sake yin sabon zaben fitar da gwani a Adamawa - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

DA DUMI DUMI Nuhu Ribadu ya nemi kotun Daukaka kara da ta baiwa jam’iyar APC damar sake yin sabon zaben fitar da gwani a Adamawa

DA DUMI DUMI Nuhu Ribadu ya nemi kotun Daukaka kara da ta baiwa jam’iyar APC damar sake yin sabon zaben fitar da gwani a Adamawa

Ranar Laraba 26th. Oktoba 2022 , Mallam Nuhu Ribadu ya shigar da ‘kara a babban kotun daukaka ‘kara dake Yola fadar jihar Adamawa inda ya roki kotun da ta bawa jam’iyar APC a jihar Adamawa damar sake yin sabon zaben fitar da gwani na gwamna

Idan dai ba a manta ba Ribadu wanda ya kasance daya daga cikin mutane 5 da suka sha kayi a zaben fitar da gwanin da akayi a ranar 27 mayu 2022 inda Sanata hajiya Aisha Dahiru Binani ta lashe zaben na fitar da gwani a matsayin ‘yar takarar gwamnan jihar Adamawa a jam’iyar ta APC a wanncan lokacin.

Wanda hakan yasa mallam Nuhu Ribadu ya garzaya kotun tarayya dake Yola inda ya kalubalanci nasarar da ita sanata Binani ta samu wanda wanan dalilin ne yasa kotu ta soke zaben fitar da gwanin na jam’iyar APC a Adamawa sanan a karshe ma dai kotun tace jam’iyar ta APC batada dan takarar gwamna a jihar a Adamawa a zaben 2023

Mallam Nuhu Ribadu yabi sahun abokiyar karawar sa sanata Aisha Binani da ma hukumar zabe ta kasa wato INEC inda ya sake garzayawa kotu kamar yadda sanata Binani da hukumar zabe tayi

Sai dai zuwan na mallam Ribadu ya banbanta da na Aisha Binani da kuma na hukumar zabe a wanan lokacin inda ya bayyana kotun daukaka kara da ta baiwa jam’iyar APC a jihar Adamawa damar sake sabon zaben fitar da gwani na wanda zai yiwa jam’iyar takarar gwamna a jihar Adamawa a zaben 2023

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button