LABARAI/NEWS
Da dumi dumi Wata jami’a a Nijeriya ta hana ɗalibai amfani da wayoyin zamani

Da dumi dumi Wata jami’a a Nijeriya ta hana ɗalibai amfani da wayoyin zamani
Jami’ar Bingham da ke Karu a Jihar Nasarawa ta fitar da sanarwar hana dalibai amfani da wayoyin zamani
Sanarwar, mai ɗauke da kwanan wata, 18 ga Janairu ta sanar da ɗalibai cewa an ɗauki matakin ne biyo bayan karya dokokin makaranta game da amfani da wayar hannu na zamani
Sanarwar ta kara da cewa Bayan karya dokoki akai-akai wajen amfani da wayoyin Hanna wanda ya saɓa wa dokar makarantar jagoranci ga dalibai an haramta amfani da wayoyin komai da ruwanka da gaggawa
Za a kwace wayoyin waɗanda su ka karya wannan doka kuma za su fuskanci hukunci da ya dace