ylliX - Online Advertising Network DA DUMI-DUMINSA Kungiyar ASUU Zata Janye Yajin Aiki, Dalibai Zasu Koma Makaranta Inji Lauyan ASUU Femi Falana - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

DA DUMI-DUMINSA Kungiyar ASUU Zata Janye Yajin Aiki, Dalibai Zasu Koma Makaranta Inji Lauyan ASUU Femi Falana

DA DUMI-DUMINSA Kungiyar ASUU Zata Janye Yajin Aiki, Dalibai Zasu Koma Makaranta Inji Lauyan ASUU Femi Falana

Babban lauya Femi Falana ya bayyana kwarin gwiwar cewa, nan ba da dadewa kungiyar malaman jami’a karkashin ASUU za su janye yajin aikin da suke yi tun watan Fabrairun bana.

Falana ya bayyana cewa, janye yajin aikin ba wai makwanni zai dauka ba, zai zo ne cikin ‘yan kwanaki masu zuwa nan kusa, kamar yadda jaridar Tribune Nigeria ta ruwaito.

Babban lauyan ya bayyana hakan ne a yau Litinin 10 ga watan Oktoba a jihar Legas yayin bikin kaddamar da littafi mai suna Breaking Coconut With Your Head da Lanre Arogundade ya wallafa.

Ya kuma bayyana cewa, akwai yiwuwar dinke duk wata baraka ta yajin aikin a wajen kotu, kamar yadda aka ba kungiyar shawari

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button