LABARAI/NEWS

DA DUMI DUMINSA Nigeria tana cikin matsala idan Tinubu ko Atiku suka Zama shugaban kasa Dattawan Arewa.

DA DUMI DUMINSA Nigeria tana cikin matsala idan Tinubu ko Atiku suka Zama shugaban kasa Dattawan Arewa.

Ango Abdullahi ya tofa Albarkaci bakinsa a game da manyan Yan takaran shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da Atiku Abubakar.

Dattijon ya nuna Babu wani Abu da Tinubu da Atiku zasu iya tabukawa akan mulki jagoran na kungiyar Dattawan Arewa ya dauki tsawon lokaci yana Gargadin Yan Nigeria akan Zaben Atiku Abubakar da Bola Ahmed Tinubu.

Ango Abdullahi yace Yan takaran APC da PDP ba zasu iya tabukawa komai ba, yace jama’a su shirya shiga matsala idan daya daga cikinsu ya lashe zabe a 2023.

Sannan ya Kara da cewa ya za’a kalli Tinubu da Atiku ayi tunanin su ne zasuyi gyara a Nigeria? Shekaru 25 zuwa 30 Kenn ana damawa dasu me suka yiwa talakawan Nigeria?

Sai dai ango Abdullahi ya jinjinawa sanata rabi’u Musa kwankwaso inda yace shi kwankwaso mutumin kirki ne, Mai karancin shekaru tare da mu, ya Fara siyasa kwankwaso jajirtaccen mutum ne Inji ango Abdullahi Allah Ya Canzama Mummuna da Kyakkyawa Kuma Yazamomana Alkhairi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button