ylliX - Online Advertising Network DA Dumi Duminsa: Za A Ƙara wa Shugaban Ƙasa, Da Gwamnoni Albashi a Nigeria - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

DA Dumi Duminsa: Za A Ƙara wa Shugaban Ƙasa, Da Gwamnoni Albashi a Nigeria

Da Dumi Duminsa: Za A Ƙara wa Shugaban Ƙasa, Da Gwamnoni Albashi a Nigeria

Hukumar tarawa da rarraba kuɗin haraji ta ƙasa ta ce ta kammala dukkan shirye-shiryen sake duba albashin masu riƙe da muƙaman siyasa, da ma’aikatan shari’a, domin dacewa da halin da ƙasar ke ciki.

A wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na intanet ta ce, a yanzu haka ana aiki ne da dokar da aka tsara tun shekarar 2008, wadda ta yi la’akari da yanayin da ake ciki lokacin da aka tsara dokar.

Sanarwar ta ambato shugaban hukumar Engr. Elias Mbam na cewa za’a sake duba albashin zababbun shugabanni da masu rike da muƙaman siyasa, kama daga shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli, da gwamnoni da kwamishinoni, da albashin shugaban ƙasa da mataimakinsa da kuma ‘yan majalisun jiha da na tarayya.

Mista Mbam ya ce haƙƙin hukumar ne ta tsara albashin zaɓaɓɓun shugabanni da masu riƙe da muƙaman siyasa, tun daga matakin ƙananan hukumomi zuwa matakin tarayya.

To sai dai a ɗayan ɓangare ƙungiyar ƙwadago ta kasar ta nuna rashin jin daɗinta game da matakin, tana mai cewa babu waɗanda suka fi cancantar ƙarin albashi a ƙasar kamar ma’aikatan gwamnati.

Kamar dai yadda Katsina Daily News ta ruwaito ƙungiyar ƙwadagon ta ce a halin yanzu masu rike da muƙaman siyasa sun fi kowa samun albashi mai gwabi a ƙasar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button