LABARAI/NEWS
DA DUMU-DUMU SA An kama wani matashi mai yin garkuwa da mutane yayin da yake cire kudin fansa a POS da ke Ondo

DA DUMU-DUMU SA An kama wani matashi mai yin garkuwa da mutane yayin da yake cire kudin fansa a POS da ke Ondo
Jami’an rundunar yan sandan jihar Ondo sun kama wani da ake zargin me yin garkuwa da mutane ne wanda ya yi garkuwa da wata yarinya yar shekara 6 a cikin motar mahaifiyarta
An ce wanda ake zargin da kungiyarsa sun yi garkuwa da yaron ne a lokacin da mahaifiyar ta ke siyan kayan abinci
Wanda ake zargin wanda ya kira iyalin wanda yayi garkuwa da su ya bukaci a ba shi Naira miliyan 50 a matsayin kudin fansa kuma an biya shi a cikin asusu banki
jami’an yan sanda sun kama wanda ake zargin ne a lokacin da yake kokarin cire kudin daga asusun bakin sa ta hanyar aikin da me POS