Latest Hausa NovelsLABARAI/NEWS

Da na zaɓi Osinbanjo a matsayin shugaban ƙasa gara na maimaita zaɓan Buhari…

Da na zaɓi Osinbanjo a matsayin shugaban ƙasa gara na maimaita zaɓan Buhari…

Jiya wani Bidiyo ya yaɗu akan cewa wai Pastor Professor Yemi Osinbanjo ya naɗa musulmi muƙamai a ofishin sa, don hakan ya ƙaryata cewa yana fifita Arna musamman ƴan cocin shi na RCCG akan musulmai..

Toh sai dai wasu takardu sun bayyana yanda mutum goma sha biyun(12) da su ka fito su kayi bidiyo don ƙaryata wancan zance da sunan cewa su ɗin Pastor Osinbanjo ne ya ɗauke su aiki, ƴan ƙalilan ne.. don kuwa acikin mutum 80, mutum 68 duk Arna ne ƴan cocin nashi na RCCG. Kuma su ma mutum 12 da su ke bawa agendar kariya yawancin su ba osinbanjon ne ya naɗasu kai tsaye ba, fadar shugaban ƙasa ce ta naɗa su sannan ta tura su aiki ofishin mataimakin shugaban ƙasa.

Ra’ayina..

Duk da cewa ina matuƙar jin ciwon yanda Buhari ya zuba mana ƙasa a ido a matsayin shi na wanda da yawan musulmi ƴan Arewa su ka marawa baya ya kai ga ci. Hakan ba zai taɓa zama dalilin da zan ajiye musulmi ɗan uwana na zaɓi pastor osinbanjo da yake nuna fifiko ƙarara akan waɗanda ba sa addini irin nasa ko kuma ƴan ƙungiyar sa.

Wataƙila shi irin nashi kishin kenan, kuma bai yi laifi ba a wajan mutanen sa. Babu mamaki muma da ace mun samu wanda zai ringa nuna mana fifiko a matsayin mu na ƴan yankin sa ko ƴan addinin da ya fito sai mu yi alfahari da shi mu danne gaskiyar adalcin da ya kamata yayiwa dukka al’umma mu kare ƙaryar fifikon da zai nuna mana.

Amma abun ba haka yake ba, ga Buhari nan ya zama misali. Na mu ne(musulmi ɗan arewa) amma nasu ne(ya zama kamar daga cikin su ya fito) ta hanyar fifita buƙatun su akan namu.

Ustazu

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button