LABARAI/NEWS

DAGA MASARAUTAN ZAZZAU

DAGA MASARAUTAN ZAZZAU:-

Mai Martaba Sarkin Zazzau kuma Shugaban Majalisan Sarakunan Jihar Kaduna Malam Ahmed Nuhu Bamalli tare da Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmed El-Rufai’i da sauran muhimman mutane daga ciki da wajen Jihar Kaduna a safiyan yau sun halarci kaddamar da shirin Bunkasa Samar da Kayyakin Lafiya na Jihar Kaduna wanda kamfanin Zipline take gabatarwa ta amfanin da jirgin Sama wanda bai amfani da matuki.
An gabatar da kaddamar da shirin ne a Garin Fambeguwa ta Karamar Hukumar Kubau a nan Jihar Kaduna.

** Mai Martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmed Nuhu Bamalli da ‘yan Majalisan Masarautan Zazzau bisa jagorancin Hakimin Gundumar Soba Uban Garin Zazzau Alhaji Bashir Shehu Idris sun gabatar da Sallan Jumma’a na yau a Masallacin dake Garin Soba wanda Liman Malam Rilwanu Kasim ya jagoranci sallan.
Bayan idar da Sallan Mai Martaba Sarkin Zazzau ya gabatar da jawabi ga Al’umma inda yai kira a gare su da su rungumi zaman lafiya taimakon juna. Sarkin ya kara da sanar da al’umman cewan nan gaba kadan zai fita domin gabatar da rangadi zuwa dukkanin Gundumomin dake Masarautan Zazzau domin ganawa da jama’a.
An gabatar da addu’a na musamman ga Mai Martaba Sarkin Zazzau bayan idar da Sallan na Jumma’a kafin ya wuce zuwa Zariya.

-#Media and Publicity Office, Zazzau Emirate with additional Pictures by Mohammed Aliyu Nata’alah and Yakubu Idris Bamalli (YAKS)

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button