LABARAI/NEWS

Dakarun Nijeriya sun hallaka ƴan ta’adda 10 tare da kwato makamai a Katsina Kebbi da Katsina

Dakarun Nijeriya sun hallaka ƴan ta’adda 10 tare da kwato makamai a Katsina Kebbi da Katsina

Dakarun Operation Forest Sanity sun kawar da ‘yan ta’adda 10 tare da kwato tarin makamai da alburusai a arangamar da suka yi a jihohin Katsina da Kebbi da Zamfara

 

a ranar Talatar da ta gabata ne sojojin su ka yi nasarar fatattakar ƴan ta’adda biyu tare da kwato bindigu kirar AK47 guda biyu da kuma wasu guda uku a wata musayar wuta da su ka yi a hanyar Maidabino zuwa Danmusa a jihar Katsina

 

Ya ce sojojin sun kuma yi arangama da ‘yan ta’adda a kauyen Dangeza a ranar Laraba, inda su ka kashe dan ta’adda daya tare da kwato bindiga kirar AK 47 guda daya da ke kan babur dauke da gidan jera alburushi guda biyu, da sauran su.

 

Dakarun sun fatattaki ‘yan ta’addan a wurare daban-daban sannan kuma an yi artabu da su bayan da sojojin suka yi nasarar kashe ‘yan ta’adda bakwai, sun kwato motoci hudu da babura takwas da suka lalata

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button