LABARAI/NEWS

Dala biliyan ɗaya muke kashe wa duk shekara don fitar da yan Nijeriya daga kangin talauci – Minista Sadiya

Dala biliyan ɗaya muke kashe wa duk shekara don fitar da yan Nijeriya daga kangin talauci – Minista Sadiya

Ministar kula da ibtila’i da jin kai Hajiya Sadiya Umar Faruk ta bayyana cewa, sun kashe Dala biliyan 7 daga hawan Shugaban kasa, Muhammadu Buhari zuwa yanzu dan fitar da daukacin ‘yan Najariya daga kangin talauci.

Tace wannan na cikin tsarin fitar da mutane miliyan 100 daga talauci da gwamnatin tarayya ta faro.

Tace shirin yana mayar da hankali ne akan mutanen da suke fama da matsalar rayuwa da kuma ke da rauni. Ya bayyana hakane a jihar Bauchi wajan kaddamar da shirin Nskills na tallafawa matasa.

Tace duk shekara Dala Biliyan 1 ake warewa dan tallafawa mutane a Najeriya, tace kuma shirin shine irinshi mafi girma da ake yi a nahiyar Afrika

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button