Daga Malaman mu

DARASI GA MATA

A wata makarantar Islamiyyah an gabatar da Walimar yayen ‘dalibai (Haflaa), sai ‘daya daga cikin Malaman da suka gabatar da wa’azi a wurin yace:

Yana koyar a wata Islamiyyah sai wani yaron da bai wuce shekaru 12 ba yaje ya same shi yace Malam ina so ka dinga yin addu’a wa Mama ta.

Sai Malamin yace me ya faru da Maman ka?

Yaron yace Mamana ta rasu kuma kullum idan na kwanta bacci da daddare sai tazo mun cikin mafarki tace “Ya kai yaro na kayi mun addu’a Allah ya sassauta mun azabar da ake mun”.

Yaron yace Mama zan miki addu’a, Allah yaji kanki ya yafe miki.

Malamin yace me ka gani ake yiwa Maman ka?

Yace nakan ganta a daure tana kuka, tace mun ana mata duka mai mugun yawa, kuma ana mata azaba da wuta a hannun ta da sauran gabobin jikin ta.

Malamin yace yaushe Maman ka ta rasu? yace tun ban kai shekaru 9 ba, yanzu ina 12.

Malamin yace Maman ka ta gaya maka laifin me tayi ake mata azaba haka?

Yaron yace:

Babana yana da mata Uku har da Mamana, yana da ‘ya’ya 7, kuma Mamana bata da wani ‘da sai ni, sauran matan su suke da yara 6.

Sai Baban mu ya sake su, Maman mu ita take kula da sauran yaran, kullum da safe idan ta hada mana Tea sai ta zuba Madaran Kofi na da yawa, sauran yaran kuma Madaran su baya kai yawan nawa.

Tace mun abinda yasa ake mata azaba kenan tun ran da ta rasu har yau.

Malamin yace sai nace ma yaron ka dinga tashi karfe uku na dare kana mata addu’a.

Kuma idan kayi karatun al-Qur’ani kar ka tashi a wurin sai kayi mata addu’a.

Yace bayan kwana biyar sai yaron yazo yace Malam jiya naga Mamana a mafarki

kukan da take ya ragu, amma har yanzu tana kukan, sai dai bai kai na baya ba.

Malamin yace sai nace masa ka cigaba da addu’a da kuma yawan karatun al-Qur’ani kana mata addu’a.

Bayan kwana biyu yaron ya sake cewa Malam naga Mamana yau kukan ta ya ragu sosai, hawaye kawai take yi, tana cewa jikin ta yana mata zafi.

Malam yace ka cigaba da addu’a kuma nima ina yi mata addu’ar.

Bayan kwana kadan yaron yazo yace Malam naga Mamana yau tana murmushi tana cewa

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button