Islamic Chemist

Don kare kanka daga cututtukan Ƙoda yana da kyau kasan waɗannan hanyoyi

Don kare kanka daga cututtukan Ƙoda yana da kyau kasan waɗannan hanyoyi:

 1. Ka riƙa shan ruwa sosai.💧
 2. Rage yawan shan gishiri.
 3. Idan kaji fitsari kayi shi ba ɓata lokaci.
 4. Daina shan magani ba bisa ka’ida ba. Kada kuma ka riƙa shan magungunan gargajiya ba tsari.
  5 Ka rage ƙunatar maiƙo ‘musamman’ in kana da ƙiba.
 5. Kada kasha giya, sigari ko shisha
 6. Kar ayi amfani da Allurar Haska fata(bleaching) irinsu Glutathione.
 7. Ka riƙa motsa jiki.
  9 Ayi ƙoƙarin shan magani idan akwai infection

-Akwai nau’in cututtukan ƙoda kala-kala amma abubuwan da muka faɗa a sama zasu taimaka wajen kariya daga mafi yawansu.

Idan anga fitsari da jini, ko rashin fitsarin ko kumburi da zafi a kuiɓin ciki daga ƙasa-kasa da zazzaɓi, aje asibiti da sauri.

Allah bamu Lafiya🙏

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Check Also
Close
Back to top button