Fadakarwa

Duk Wani Magidanci Ya Dace Ya Fahimci Hakan

Duk Wani Magidanci Ya Dace Ya Fahimci Hakan

Ba kawai maza magidanta su karanta su ko su tsaya kallon hotunan dake wannan darasin ba. Ina so ne maza ma’aurata suyi amfani da darasin domin gayara Zamantakewar aurensu.

Hakan nan kuwa yana da kyau duk wani magidanci ya fahimci cewa, abunda wata macen take so ba shi ne wata macen take son ba.

Sai dai ga wasu abubuwan da ya kamata duk wani magidanci ya sani.

1: Duk wata mace tana son mijinta ya kasance shine Jagoran gidansa.

2: Duk wata mace tana son mijinta ya taimaka mata wajen tarbiyan yaransu da suka haifa.

3: Duk wata mace tana son mijinta ya maidata gimbiyarsa wajen girmamawa da mutuntawa.

4: Duk Wata Mace tana son taga mijinta yana shawara da ita.

5: Duk Wata mace tana son ganin mijinta na alfahari da ita.

6: Duk wata mace tana son taga mijinta na alfahari da ita a gaban abokansa da kawayenta.

7: Duk wata mace tana son ganin ta samu kusanci da mijinta.

8: Duk wata mace tana son taga tana samun lokacin yin hira da mijinta.

9: Duk wata mace na son taga mijinta yafi kowa fahimtar ta.

10: Duk wata mace tana son taga soyayyar da mijinta yake mata shike motsa mata sha’awa.

Da fatan maza magidanta zasu daure su rika yiwa matansu wadannan abubuwan harma da kari.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button