LABARAI/NEWS

DUNIYA INA LABARI

Za a ji yadda dubun wani mahaifi za cika bayan da ya kashe yaransa 3, sannan ya boye gawarsu cikin firiji.

A Kano kuwa, an yi rashin dacen makwabci, sakamakon yadda wani matashi ya yi wa ‘yar makwabtansa yankan rago.

Wata fusatacciyar budurwa ta bude shafukan Instagram har guda 30, kawai don jefa tsohon saurayinta cikin jalala ta hanyar tura sakonnin barazana da sunansa.

A gefe guda kuma, wani saurayi ya tsohuwar budurwarsa rena kallon fuskarta a madubi, bayan da ya lakdamata dan karen duka har ya rusa mata hanci da baki.

Wani dan majalisa a Kamaru ya gamu da ajalinsa, bayan da wasu ‘yan bindiga dadi suka bude masa wuta.

Zakaran dan wasan tennis, Novod Djikovic, ya amince da karya dokokin shiga kasar Autraliya bayan da maganar ta gai kaban kuliya.

Za a ji karin bayani a cikin shirin da misalin karfe 9 na dare agogon Najeriya da Nijar….

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button