DUNIYAR NAN KWAI BAN TSORO

DUNIYAR NAN KWAI BAN TSORO
Kusan kullum na wayi gari sai na riski wani sabon al’amarin dake karamun bita game da duniya. Nide kam na gama gamsuwa duniyar nan babu wani dadi cikinta ballantana ya rudeka matukar kana da hankali zaka karanci haka.
Wato baiwar Allah ce matashiya me kimanin shekara 27 na risketa cikin (ICU) na asibiti bayan na shiga wato Intensive Care Unit kamar kace 6angaren marasa lafiyar dake bukatar cikakkiyar kulawa domin suna kan gargara ne na tsakanin mutuwa da rayuwa…. wanda kaso 95% dama basu cika dawowa ba saide su wuce lahira.
Na riski matashiyar me ya’ya 2, cikin ya’yan yar babbar mace ce inajin 4yrs, dayan kuma karamin goyo ne namiji duk kananu….. tana fama ne da ciwon hanta (LIVER CIRRHOSIS).
Kamar yadda muka sani ciwon cancer, ciwon koda, hanta, suna da mataki tundaga STAGE 1 har zuwa STAGE 4 yawanci in angano a matakin farko akan iya magancewa saide in akwai abunda yasa hakan yaci tura.
Ita abun ya riga ya jima already tana END STAGE LIVER DISEASE ma’ana tazo matakin karshe, ba abunda likitoci zasu iya yi su ceto ta saide in gudummawar hanta aka samu daidai da ita shine za’a iya mata dashe.
To ina….! A irin wannan stage din babu ma wanda ya mutum ballantana ya bata kuma koda ma ansamu ba lallai ta hau jikinta ba tunda muna samun Rejection ya zamto sassan da aka dasama mutum ainishin garkuwar jikinsa take yakar organ din domin zata dauka ciwone haka zasuita yaki har ta kashe organ din ta lalata….. wannan yasa duk wani wanda akai masa dashe na wani abu ajikinsa zaka samu ba dashen ba amma ana hadashi da magani da kullum zai rika sha saboda wancan rejection din har iya tsawon rayuwar sa kaco kan. Inba haka ba to liqi zai tashi matukar yaki shan wancan maganin.
A halin yanzu mara lafiya daya ne wanda yai fatan da zai yiwu zai bata to saide shima ciwon cancer garesa kuma cancer din ta yadu har izuwa hantarsa don haka ba hali.
Ikon Allah kenan kyakyawar mace, uwar na yaba halinta atleast, mijin ma ya yaba, yai kuma iya kokarinsa…. saide ita ahalin yanzun gata akwance batasan ma meke tafiya aduniya ba. Domin anyi sedating dinta maana angusar da tunaninta saboda da zata farko nishi zakaji tana yi mai ban tsoro tunda bama ta da karfin da zatai ihu, sannan ga yunwa tunda hanta ita ke narka abinci ita ko anbata din ma saide ya kara damula alamura ba abunda zai narkar dashi aciki…. ta karin ruwa kuma shima ina aka sa akwai matsala saide kurum ade mata maleji ya zamto babu karancin ruwa ajikinta “””inalillahi wa’inna ilayhir rajiun””
Kai mutane muji tsoron Allah kunji billahil azim wannan duniyar abar banza ce.
Tashin hankalin yanzu karfin mijin da iyayen sun kare, mijin bashi ya kar6a har ya rasa ma wanda zai kuma kara masa… ita kuma gashi dama bata iya shakar iska saboda huhun ya saki…. da Oxygen ta dogara itace tunda ta kwanta yau sama da sati ake kirgawa akalla duk awa daya zuwa biyu kudin sunkai dala $100, kimanin dubu 36 a kudin Nigeria duk awa 1 zuwa 2.😥
Don haka yanzu family din suna tattaunawa karfinsu ya kare sun sami taimako shima ya kare asayen oxygen duk abun ya tafi… don haka zasui mata abunda na ta6a fada muku wato EUTHANASIA wato Death with Dignity da ake cewa ASSITED SUICIDE tunda dokar kasa ta amince musu ta hanyar wani nata zai sa hannu ya cire OXYGEN dindaga fuskarta daga nan saita fara kokarin farauta iska (GASPING) inyaso sai jikin ya kara mutuwa shikenan babu iska sai mutuwa..
Saboda basu da kudin cigaba da wahala da ita.
Abunda ke mun yawo araina shine ina ma ace tana cikin hayyacinta tasan ina tsaye akanta…. wlh da sainai kokarin bata kalmar shahada duk da naga mahaifiyarta mai fahimta ce… duk da nasan hakan ka iya sa6a ka’ida… duk da nasan ba dole Allah ya yafe mata ba tunda kamar akan gargara take to amma ai Allah “liman yasha’u” yace inyaso sai ya gafarta mata.
A irin wannan wahalar data sha ace ka mutu ba imani akwai tashin hankali duk da nasan su abunda suke hange daban amma ni nasan ba wani peace ga wanda ya mutu ba a musulunci ba.
Toh saide ba yadda na iya, batasan ma me ake ba. Abunda na bari wani waazi ne Allah yake mun ni akaran kaina cewa na kara rike musulunci da kyau sannan na kara jin tsoronsa, haka kila wani inyaji wannan labarin ya kara gyara alakarsa da Allah
Allah ka rabamu da wahala yayin mutuwa ka tsare mu muggan cutukan da zasu durkusar damu har mu rasa yadda zamui saide jiran lokaci. Allah ka kashe mu cikin musulunci amin…