Fadar Shugaban kasa ta mayar da martani wa Nasiru El-Rufai ta bakin Ministan yada labarai lai Muhammad

Fadar Shugaban kasa ta mayar da martani wa Nasiru El-Rufai ta bakin Ministan yada labarai lai Muhammad
Gwamnatin tarayya ta mayar da martani kan ikirarin da Nasir el-Rufai, gwamnan Kaduna
ya yi na cewa akwai wasu mutane a fadar Aso Rock da ke yaki da jam’iyyar APC
Tun a ranar Larabar da ta gabata ne El-Rufai ya yi zargin cewa wasu mutane a cikin gwamnati ba su ji dadin sakamakon zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar APC ba don haka suke kokarin ganin jam’iyyar ta samu faduwa a zabe mai zuwa
Yawancin mutanen Villa ba yan jam’iyyarmu ba ne A Cewar Malam Nasiru El-Rufai Na yi imanin akwai wasu mutane a cikin Villa da ke son mu fadi zabe saboda ba su da hanyarsu
Suna da ‘yan takararsu kuma ‘yan takararsu ba su ci zaben fidda gwani ba kuma ina ganin har yanzu suna kokarin ganin mun fadi zabe kuma suna fakewa da burin shugaban kasa na yin abin da yake ganin ya dace