LABARAI/NEWS

Faransa ta umarci ma’aikatan matatar mai da su janye yajin aiki

Faransa ta umarci ma’aikatan matatar mai da su janye yajin aiki

A yau Laraba ne gwamnatin Faransa ta umarci ma’aikatan matatar mai da ke Normandy da su koma bakin aiki yayin da ta ke kokarin dakile yajin aiki a kan albashi sakamakon karancin man fetur a kasar.

Mai magana da yawun gwamnati, Oliver Véran ya ce umarnin Firaminista Élisabeth Borne ya shafi matatar mai ta Port-Jérôme, amma kuma ana iya amfani da matakan da suka wajaba a matatar mai ta biyu a Dunkirk.

Véran ya ce, “Illar rikicin ma’aikata ya zama abin matsala ga yawancin Faransawa,” in ji Véran, yana mai jaddada cewa mutane za su sha wuya wajen yin tafiye-tafiye, zuwa aiki, yin sayayya ko kai yaransu makaranta.

Kimanin kashi ɗaya bisa uku na gidajen mai na Faransa na fuskantar karancin mai bayan yajin aikin makonni biyu Direbobi suna yin layi ko tuƙi zuwa wasu garuruwa don neman mai.

Shida daga cikin matatun mai 7 na kasar sun fuskanci yajin aikin ne a daidai lokacin da kungiyar CGT ta Faransa ke yunkurin kara albashin kashi 10 cikin 100 a duk fadin matatun mai na kamfanin Total Energy.
A yau Laraba ne kamfanin Total zai tattauna da kungiyoyin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button