ylliX - Online Advertising Network Farauta Sana'a ce ta tuntuni wadda aka gada tun iyaye da kakanni - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Farauta Sana’a ce ta tuntuni wadda aka gada tun iyaye da kakanni

Farauta Sana’a ce ta tuntuni wadda aka gada tun iyaye da kakanni

Kuma farauta ita ce sana’a ta faro a kasar Hausa kafin zuwan wasu sana’o’in kamar su kiwo, noma, Su, da dai sauran sana’o’i

Mafi yawanci maza ne aka fi sani da sana’ar farauta, suna shiga daji don farauto dabbobin daji, ko da yake ana samun kadan daga cikin mata masu kamar maza suna fita farauta.

Ana amfani da makamai kamar su wuka, adda, takobi, barandami, tsitaka, gariyo, kwari-da-baka, bindiga, kulki, gora, kokara, kaho, kere, ruzu, buzu,
da sauransu.

Mafarauta suna da kidansu ta musamman wadda sukeyi idan suna farauta kamar irin su gangi da sauransu Wasu suna farauta dan nishadi wasu kuma sunayi a matsayin sana’ar da suka gada tun iyaye da kakanni

Yanxu yan Aji mu dauka nabawa kowa makaman farauta, kowa ya shiga daji ya nemo nama.
Me zaka iya kamowa?
Me zaki iya kamowa?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button