ylliX - Online Advertising Network FASTON DA YA CE EL-RUFAI YA KUSA MUTUWA, YA TSALLAKE RIJIYA DA BAYA - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

FASTON DA YA CE EL-RUFAI YA KUSA MUTUWA, YA TSALLAKE RIJIYA DA BAYA

FASTON DA YA CE EL-RUFAI YA KUSA MUTUWA, YA TSALLAKE RIJIYA DA BAYA!

Pasto Johnson Suleiman ya tsallake rijiya da baya, bayan da wasu ‘yan bindiga suka bude masa wuta a yau Juma’a a garin Auchi da ke jihar Edo, a kudu maso kudancin kasar nan.

An ga motarsa ta yi kaca-kaca da ramukan harsasai a jikinta, zuwa lokacin hada wannan rahoton ba a samu wani cikakken bayanin yadda lamarin ya faru ba.

Idan dai za a iya tunawa a shekarun baya, lokacin da Gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya sanya dokar kayyade wa’azi a jihar ne aka ruwaito Pasto Suleiman din yana yi wa gwamna El-Rufa’i barazanar cewa nan ba da dadewa ba zai mutu.

Sai dai a lokacin Malam Nasir din bai yi ko gezau ba, karshe ma sai ya ce a fada wa faston idan ya isa ya fadi ranar mutuwar hade da lokaci, tunda mutuwa dole ce ga kowa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button