Fadakarwa

GAGGAUTA AIKIN ALKHAIRI AKE, SABODA RAYUWA BA TABBAS

GAGGAUTA AIKIN ALKHAIRI AKE, SABODA RAYUWA BA TABBAS

Malam ke cewa: A musulunci an hana gaggawa saboda aikin shaiɗan ne, saide akwai inda akai togaciya wato guraren da aka buƙaci mutum yai gaggawa.

 1. Idan mutum na aikata zunubi toh daga randa ta bayyana masa cewa wannan abin ba abune mai kyau ba toh anason yai gaggawa ya tuba ya dena. Saboda jinkirta tuba abune me matukar hatsari.
 2. Sannan idan ana bin mutum Bashi, toh kana samun abin biya anaso ka gaggauta biya. Kada ma mutum ya tsaya wata-wata ko tunanin wasu bukatu nasa, yai Maza ya biya bashi kurum.

Domin jinkirin bashin me wadata zalunci ne. Duk wanda ake bi bashi alhalin yana da abin biya amma yaƙi to da shari’a za’ai hukuncinsa yana hannun gwamnati “CRIMINAL OFFENCE”ne, ya zama laifi tunda annabi ya ambaci hakan da zalunci; “Maɗulul-gani zulmun”
jinkirin bashin me wadata zalunci ne.

 1. Idan kana da ƴa Mace ta isa aure, ta kuma nuna tanaso kuma ga masu sonta sun bayyana to anaso ka gaggauta aurar da ita.
 2. Idan Mutum ya mutu toh ai gaggawar masa sutura aje binnesa.
 3. Idan kai Baƙo toh kai gaggawar saukarsa. Wato Baƙo na zuwa inde kasan baƙunta karka fara kai masa ruwa ko abinci… A’ah fara nuna masa gurin kewayawa (Banɗaki) ta yiwu a matse yazo!
  Inyaso yana tafiya banɗakin kafin ya fito kai kuma ka shirya masa abinda ya sauwaka. Da ya fito saide ya tarar da ruwan sanyi, ko lemo, ko abinci daki-daki na mutuntawa. Shiyasa anan ma gaggawa ake so.
 4. Zuwa Makaranta neman ilimi shima gaggawa ake. Ma’ana idan har mutum yasan ga inda makaranta take ta samun ilimi toh yai gaggawa, banda jinkirin cigaba da zama da jahilci mutum ya riqa sai lokaci kaza.
 5. Duk abinda ake bukata na ibadah ko kyakyawar mu’amala ko biyayya toh inya taso yi sauri kayi, kada ka zauna kace sai lokaci kaza tukun.
  Domin nawa akayi amma kafin lokacin basu da rai! don haka lokaci ake sallata. Damar kayin da dalilin duk yana hannun Allah idan ya canzasu shikenan. Ko menene indama ta samu ba’a jinkiri.

┈┉━┅━💕🌷💕━┅━┉┈

Sannan Annabi Alaihi salam ya sanar damu: BAADIRU BIL A’AMALI SABA’AN .

Kullum ɗan Adam na rigima ne da abu guda bakwai “7” suna kaiwa da komawa a tsakaninsa, kana yawo suna yawo, toh kafin a haɗun kai maza kai abinda ya kamaceka. Yace;

 1. HALTAN’TAZIRUNA ILLA FAQARAN MUNSI’AN:

Daga abin da ɗan adam ke cikin hatsarin kiciɓis dashi kwai “talauci irin Mesa Mutum ya Manta komi sai cikinsa. “🥲
Watakila Mutum zai gamu da wannan don haka Kafin a haɗun abinda kake dashi yi sauri kayi na alkhairi.

 1. AU GI-NAN-MUƊI’GIYAN:

Ko kuma wadata maɗuɗiya, arziki me tarin yawa da zaisa Mutum bai isa yai sallah cikakkiya bama, ballantana yinta natse saboda ruɗewa da tunane-tunanen dukiya, Watakil sallar saida direba me ankarar dashi ana masa tuni cewa yanzu a raka’a ta kaza kake alhaji,
Sannan sada zumunci zai wuya, tashi ai ƙiyamul layl zai wuya, karanta kur’ani zai wuya, cin abinci ma zai wuya, bacci ma wadatacce zai wuya duk saboda harkokin dukiya.
Annabi yace Mutum yai sauri ya tara ibadu kafin irin wannan ta riskesa saboda in irin wannan ta samu bayan ya riga yai aiki toh yaci riba.

 1. AU -MARDAN MUBSIDAN:

Ko rashin lafiya me kassara ɗan adam. Mutum ya zamo baya motsi saide akwantar atayar, ko baya iya magana, ko kuma taɓin hankali da zaike cire tufafinsa har sai ankamasa ansa masa, ko ya ringa cin Najasa saboda kai ya juye.
Sai annabi yace toh nan ma mutum yai kokari yai aiki watakil wannan zata iya samunsa kafin tazo ya gama tara ibadu.

 1. AU- HARAMAN MUFINIDAN:

Ko kuma tsufa Me sa amingiye! Wato mesa rikicin kwakwalwa, Mutum na iyayin bawali azaune amma ya rika kururuwar azo ataimakeshi ga maciji nan yana binsa, ko kuma bai faɗi magana ba yace ya faɗa, haka za aita rikici da mutum.

Mutum yana zaune agidansa amma ya riƙa kukan azo akaishi garin su. Annabi yace watakil Mutum ya haɗu da irin wannan. Don haka yi kokari ka mori kuruciya kai aiki tuƙuru domin inbakai yanzu ba in tsufa yazo bazaka iya komi ba.

 1. AU MAUTAN MUHUJIZAN

Ko Mutuwa mai fuf ɗaya, wacce zata tumɓuke mutum ta ciresa har saiwarsa… Yai gaba bai bar kowa ba, Me yankakken baya.

Don haka inka sami sukunin aure yisa akan lokaci, inkana wasa da sallah ko sadaka ko ibadah kiyayi kanka, haka inka sami damar gina sadakatul jariya bari kallon kudin yi maza kai abinda ya dace kafin wannan ta faru gareka…
.
Saboda intazo mutum bai komi ba abinda zaice shine: “RABBI LAULA AKHTARTANI ILA AJALIN QARIB”
Wato ya Allah kai mun jinkiri ɗan lokaci ƙanƙani koda na minti guda.

Saboda duk ƙunzugurmin jahilcin Mutum ranar da mutuwa tazo zai gane wani abu na daga muhimmancin SADAKA!
Shiyasa daga hujjar da zai kafa shine “FA ANSADDAQA WA’AKUNA MINAS SALIHIN” kai mun jinkiri zan sadaka don na zama daga cikin mutanen kirki… Saboda a lokacin anyaye masa hijabi ya shiga “FAKASHAFNA ANKA GIƊA’AKAAH FABASURUKAL YAUMA HADEED” Ya gane cewa Mutuwa zai, gashi saida lokaci ya qure ya fahimci
“Assadaqatu taqimus sariqas suq”
Sadaka na hana Mummunar mutuwa shi kuma yasan mutuwar zai ba fashi domin Allah ya dosa gaba gaɗi…toh inda za’a bashi damar sadaqar inyai yasan zata hanasa mummunar mutuwa.
.
(SADAQATU TUƊIQI’U GADABAR RABB) sadaka ke shafe fushin Allah kamar yadda ruwa ke kashe wuta. Shyasa komi jahilcin Mutum inya sha tafi qarfin cikinsa wannan damar zai roka abashi inyazo mutuwa bisa kuskure.

Don haka wanda yake da rai ayanzu sai ya dage yai iya kokarin gwargwadon abinda zai na sadaka, ba ruwanka da wanda kake ba kila sun fika kuɗi, kaide nufaci Allah da ita komi ƙanƙantarta.

 1. AU WID’DAJ’JAL BASHSHARU GA’IBAN YUN TAZAR’RU

Ko zuwan dajjal! Shine mafi sharrin wanda baya nan ake sauraren zuwansa Allah ya karemu.

 1. AU WIS SA’AT

Ko tashin qiyama, wacce annabi saida yai mata kirari itama yace; “Wassa’atu Adaha Wa Amar”….
Wato alkiyama itace mafi gigitarwar masifa kuma mafi ɗacin bala’i.

Haka zata zo wani yana kasuwa, wani ya zira guga arijiya yana me jan ruwa, wani na kuka, wani na dariya, wani na aikata zina, wani na tuqi a mota, wani na bacci, wani na makaranta, kowa de yana abinda yake… Saide kurum aji Futt anbusa ƙaho, shikenan kowa ya Mace.

Allah yasa mudace.

GAGGAUTA AIKIN ALKHAIRI AKE SABODA RAYUWA BA TABBAS

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button