LABARAI/NEWS

GANIN JINI BAYAN JUMA’I KADAN KO LOKACIN SADUWA NADA ALAKA DA DAYA DAGA CIKIN WADANNAN DALILAI

GANIN JINI BAYAN JUMA’I KADAN KO LOKACIN SADUWA NADA ALAKA DA DAYA DAGA CIKIN WADANNAN DALILAI

Idan mace na ganin jini lokacin ko baya saduwa to akwai daya daga cikin wadannan dalilai.

  1. Kusantar al’ada, lokacin al’ada ko ovulation ko kuma alamun kyankyanshewar kwai.
  2. Alamar farko farko ta PID Wato wato pelvic imflammatory disease.
  3. Alama ta wasu daga cikin STIs wato sexual transmitted infections.
  4. Rashin wadatattar ni’ima ga mace, ko karancin tado da sha’awa lokacin saduwa ya Kamata ace an samu wasa Mai zurfi ta Yanda sha’awa Zata motsa sosai kafin saduwa.
  5. Karcewa ko jin rauni a gaba lokacin saduwa musamaman idan ana anfani da hannu lokacin juma’i idan akwai farce a yatsu yana karce wata karamar blood vessels jini ya rika fita.

Lokacin da aka hadu da matsala kafin magani ko daukan mataki akwai bukatan cikakken bayani ga likita ta yanda za a gane hanyar magance matsalar.

ALLAH YA KYAUTA
KABIRU DANWURI

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button