ylliX - Online Advertising Network Ghana ta kori 'yan Najeriya 16 da aka kama suna aikata Zambo ta yanar gizo - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Ghana ta kori ‘yan Najeriya 16 da aka kama suna aikata Zambo ta yanar gizo

Ghana ta kori ‘yan Najeriya 16 da aka kama suna aikata Zambo ta yanar gizo

Dokta Chukwu Emeka, Konturola na rundunar ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a garin Seme na jihar Legas.

Hukumar kula da harkokin kudi da leken asiri ta Ghana ta zarge su da aikata laifuka ta yanar gizo amma daga binciken mu na farko, mun gano cewa wasu daga cikin su an ruguza su cikin wadannan ayyukan ta’addanci saboda matsalar rashin wadatar arziki da matasanmu ke fuskanta.

Wasu daga cikin su abin ya shafasu ne ta hanyar yaudarar su cewa za su iya samun kudi idan sun bar Najeriya. Abin takaici, ba su sami ainihin abin da suka yi ciniki a Ghana ba.

Bincike ya kuma nuna cewa mafi yawansu sun bar kasar ne ta hanyoyin da ba su dace ba ko kuma ta cikin teku zuwa wasu kasashen yammacin Afirka.
Mun kuma gano cewa yawancinsu sun yi balaguro ne ba tare da sahihan takardun tafiye-tafiye ba, don haka da suka isa Ghana suka zama ganima ga hukuma.

Daya daga cikin wadanda aka kora, Richard Paska, dan shekara 24 da ya kammala karatunsa na jami’ar Nnamdi Azikiwe, ya ce an yi masa alkawarin zuwa Ghana ne da alkawarin samun kyakkyawan aiki.

Dole sai da mahaifina ya nemi kudi don ya bar ni a watan Fabrairun 2021, domin in fara aiki. Aikin kuma na intanet, amma da na isa Ghana, labarin ya canja.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button