Latest Hausa Novels

Gobara: Wuta ta tashi a F.C.E Zariya

Gobara: Wuta ta tashi a F.C.E Zariya

Daga Mustapha Muhammad Rajab

A Rahoton da muka samu da misalin ƙarfe 10:05am na safiyar yau Asabar ne wata wuta da ba a san menene dalilin kamawarta ba ta tashi a Computer Department F.C.E Zariya.

Wakilinmu ya zanta da ɗaya daga cikin ɗaliban makarantar, Ni dai ban san farkon abin da ya faru ba saboda ina aji akace ai gobara ta tashi, shi ne muka fito muka tarar wutar tana ci. bayan mun fito ba tare da daɗewa ba sai ga motan kwana-kwana, suna zuwa ba tare da ɓata lokaci ba suka fara kashe wutar da ta kama.-Inji ɗalibar mai suna A’ishat S. Naseer. ta ci gaba da cewa.

Amma gobarar lab ɗaya ta ci, kuma lab ɗin Practical ne akwai computers da yawa a ciki, A saman bene ne kuma ya ƙunshi ajujuwa biyu, sai offices, sai lab biyu, Amma zancen gaskiya waɗanda suke gurin sun ce suna aji kawai suka ga hayaƙi na tashi hasalima lab ɗin a kulle yake da mukulli ba kowa a ciki.
-Inji A’ishat S. Naseer ɗaliba a F.C.E Zariya.

A yayin kammala haɗa wannan Rahoton mun samu tabbacin wutar bata ci rai ko ɗaya ba, sai dai asarar dukiya da aka samu a gobarar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button