Islamic Chemist

GORUBA ( DOUM PALM FRUIT)

GORUBA ( DOUM PALM FRUIT):

Goruba na dauke da sinadaran Nutrition kamar haka:

 • Protein
 • Fiber
 • Amino acid threonine
 • Carbohydrates
 • Calcium,
 • Magnesium,
 • Potassium,

Haka kuma tana dauke da sinadaran:

 • H. thebaica ( Wanda ake amfani da ita wajen magance hawan jini)
 • hematinic agent (Sinadaran karin jini irin su iron da sauran su)
 • flavonoid ( wannan sinadarin yana taka rawa wajen daidatuwar suga)

Goruba na dauke da sinadarai diyawa wanda baza mu iya lissafa su ba.

Abu me amfani shine menene amfanin ta a jikin Dan adam kuma ya za’ai amfani da ita.

Ga kadan daga cikin amfanin ta da yadda za’ayi amafani da ita:

 1. Masu fama da cutar asma za su iya shan garin kwallon goruba a cikin tafashashen ruwa.
 2. Yana taimakawa masu samun matsala lokacin fitsari.
 3. Shan garinta a ruwan dumi na taimakawa masu karancin jini a jiki.
 4. Goruba na maganin matsalar hawan jini.
 5. Haka zalika goruba na magance cutar basir.
 6. Yana kuma kare mutum daga kamuwa da cutar daji.
 7. Cin goruba na kara karfin namiji.
 8. Yana kuma rage kiba a jiki.
 9. Cin goruba na kara karfin kashi da hakora.
 10. Ruwan jikakkiyar goruba na tsiro da gashin mutum idan dai aka wanke kai da shi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Check Also
Close
Back to top button