ylliX - Online Advertising Network Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle, Ya Kalubalanci Tare Da Gargardin Hukumar EFCC Kan Yunkurin Bata Masa Suna - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle, Ya Kalubalanci Tare Da Gargardin Hukumar EFCC Kan Yunkurin Bata Masa Suna

Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle, Ya Kalubalanci Tare Da Gargardin Hukumar EFCC Kan Yunkurin Bata Masa Suna

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle, ya bawa EFCC dama akan su shiga duk inda sukeso domin binciken duk abunda suke son bincike akansa da Gwamnatinsa, da duk inda yake da kaddara a duniya.

Gwamnan ya kalubalanci EFCC akan wani labarin kage da karya wanda jaridar karya da sharri ta Sahara Reporters ta watsa cewa anboye wasu makudan kudade awasu wurare domin biyan ma’aikatan gwamnatin Zamfara albashi ta tsarin “Table Payment” wanda daga shugaban Hukumar EFCC kalaman suka fito.

 

 

Gwamna Matawalle ta hanyar babban Lauyansa Mike Azkhome SAN, ya rubutu dogowar takarda ga shugaban Hukumar EFCC, akan yana gargardinsu da su kare kansu kuma su bincike duk inda kaddarar shi take da kuma duk inda suke tunanin anboye kudaden al-umma, haka zalika Gwamnan ya gargardi hukumar EFCC akan su daina yunkurin bata masa suna ko ko kuma bayarda kafa ga ‘yan adawar siyasar sa akan cimma wata manufa tasu ta siyasa akan kazafi, karya da kage gareshi da Gwamnatinsa.

Gwamna Bello Matawalle, yace duk lokacinda suka tashi binciken nasu zai hadasu da mutane aminansa guda ukku domin su saka ido akan yanda EFCC zasuyi aikinsu domin kaucewa yaudara da kuma zamba cikin Aminci.

Gwamna Bello Matawalle yace ya zama dole EFCC su aiwatarda binciken ko kuma yanemi hakkinsa gaban kuliya akan kokarin bata masa suna a idon duniya amatsayinsa na dan Adam dan kasa mai cikkaken hakki. Haka kuma dolene ya barrantarda Gwamnatinshi wajen maka hukumar EFCC kotu domin neman hakki.

Gwamnan yace yayi mamaki matuka akan irin yanda hukumar EFCC ke Furta kalamai ba tare da tabbatarda gaskiyar lamari ba wanda hakan zai kawo shakku ga ingancin hukumar EFCC ga Al-umma.

Gwamna Matawalle, yace yana jira yaga dukkannin matakin da hukumar EFCC zata dauka akan kodai su fito su bayyana yadda lamarin yake akan gaskiya ko kuma ya garzaya dasu kotu domin neman hakkinsa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button