ylliX - Online Advertising Network Gwamnatin Buhari ta miƙa Shugaban IPOB Nnamdi Kanu Zuwa kotun ƙoli ta ƙasa. - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Gwamnatin Buhari ta miƙa Shugaban IPOB Nnamdi Kanu Zuwa kotun ƙoli ta ƙasa.

Gwamnatin Buhari ta miƙa Shugaban IPOB Nnamdi Kanu Zuwa kotun ƙoli ta ƙasa.

Gwamnatin tarayya ta tafi kotun ƙoli, ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin sakin shugaban IPOB, Nnamdi kanu.

Gwamnatin Shugaba Muhammad Buhari ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke na sakin shugaban kungiyar ƴan aware Biafra (IPOB), Nnamdi kanu.

Gwamnatin a wani ƙudiri na zaman zartarwa da ta shigar ranar Laraba a kotun ƙoli ta ƙasa tana neman kotun ta dakatar da zartar da hukuncin kotun ɗauka ƙara na 13 ga watan Oktoba.

Kotun ɗaukaka ƙara ta kwace shugaban IPOB kuma ta hana duk wata kotu mai karancin karfi ɗaga ƙara tuhumar da ake yi masa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button