LABARAI/NEWSLatest Hausa Novels

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Ganduje ta haramta shan Shisha, zuwan yara Hotel, luwadi madugo kuma ta kafa dokokin taron shagalin biki

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Ganduje ta haramta shan Shisha, zuwan yara Hotel, luwadi madugo kuma ta kafa dokokin taron shagalin biki.

Daga Salisu Muhd Mati

Gwamnatin ta kuma bayyana cewa daga yanzun wajibi a kulle ɗakin taro kafin 11:00 na dare, ta hana cakuduwar maza da mata.

Gwamnatin Kano ta haramtawa yara shiga otal, yin iyo tsakanin maza da mata a tafki daya.

Kwamitin ya kuma yi nazari kan dokokin da ke kula da otal-otal, gidajen abinci da wuraren gudanar da bukukuwa a jihar.

Shugaban kwamitin, Baffa Babba Dan-agundi ne ya bayyana hakan bayan wani taro da masu gidajen otel da gidajen cin abinci da wuraren taro domin sanar da su wannan sabon ci gaban da aka samu.

Kwamitin ya sanar da su wani sabon harajin da gwamnatin jihar ta yi wanda zai taimaka wajen tsaftace wuraren sana’o’insu da nufin kaucewa ayyukan karuwanci a jihar.

An kafa kwamitin ne a karkashin dokar yawon bude ido ta jihar.

“Daga cikin dokokin mue shi ne hana yara masu karancin shekaru shiga otal ba tare da iyayensu ba, hana shan Shisha, yin iyo tsakanin maza da mata a tafki daga, madigo da ayyukan luwadi.

“Kwamitin zai kara sa ido kan ayyukan DJ a wuraren bukukuwan aure da wuraren taron. Ya kamata a rufe duk wuraren taron da karfe 11 na dare,” in ji shi.

Jim kadan bayan wani taro da aka yi a gidan gwamnati, Gwamna Abdullahi Ganduje ya kaddamar da motoci sama da takwas domin gudanar da ayyukan kwamitin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button