GWAMNATIN JIHAR LAGOS TA AIKEWA DA ƳAN-KASUWAR ALABA RAGO TAKAR TADASU DAGA KASUWAR…

GWAMNATIN JIHAR LAGOS TA AIKEWA DA ƳAN-KASUWAR ALABA RAGO TAKAR TADASU DAGA KASUWAR…
Bayan zaman sasanci na tsawon watanni tsakanin Gwamnatin Jihar ta Lagos da Ƴan-kasuwar yanzu dai Gwamnatin ta basu ƙwanaki Goma Sha Hudu dasu ficce daga Kasuwar, Rundunar Ƴansanda ce dai da akafi sani da Rapid Response Squad a turance tare da Lagos Taskforce, sune suka liƙa tardar Sanarwar tada kasuwar.
CSP Olayinka Egbeyemi ya bayyana cewa bisa ga rahotannin sirri da hukuma ta samu ya bayyana cewa kasuwar Alaba Rago ta tara Ƴan Ta’ada masu cin karen su ba babbaka, da haka ne Gwamnatin Jihar ta yanke Shawarar gyara kasuwar zuwa ta zamani.
Ya ƙara da cewa ko satin da ya gabata Rundunar Ƴansandan Jihar ta gano bindigogi a yankin dama masu safarar Miyagun Ƙwayoyi dake safarar su daga yankin zuwa sauran sassan jihar ta Lagos.
Idan dai ba’a manta ba a jiya ne Gwamnatin Jihar ta Lagos ta bayyana hana amfani da baburan achaba ko Okada a wasu ƙananan Hukumomin Jihar.