LABARAI/NEWS

Gwamnatin Kaduna ya ƙaryata rahoton kai hari kan titin Abuja-Kaduna

Gwamnatin Kaduna ya ƙaryata rahoton kai hari kan titin Abuja-Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna a yau Alhamis ta karyata rahoton harin da aka ce an kai kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, a wata sanarwa da ya fitar a Kaduna, ya yi watsi da rahoton da cewa karya ce da kuma son tashin hankali.

 

 

“An jawo hankalin gwamnatin jihar Kaduna kan wani sako da ake ta yawo na cewa wai ƴan bindiga sun rufe hanyar Kaduna-Abuja.

Ya kara da cewa “Gwamnatin jihar Kaduna na mai karyata wannan sakon tare da shawartar ƴan kasa da su yi watsi da wannan mummunar dabi’a.”

Aruwan ya ce gwamnati na ci gaba da tuntubar jami’an tsaro a yankin baki daya tare da sanin halin tsaro a kan hanyar da sauran wurare.

Ya yi Allah-wadai da masu yada labaran karya, yana mai cewa ta’adar da su ka dauka wa kansu abin takaici ne matuka, kuma da gangan aka shirya su domin lalata sadaukarwar hukumomin tsaro da gwamnati.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button