ylliX - Online Advertising Network Gwamnatin Najeriya Ta Kashe Biliyoyin Daloli Wajen Biyan Kudin Makarantar Dalibai A Kasashen Waje, - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Gwamnatin Najeriya Ta Kashe Biliyoyin Daloli Wajen Biyan Kudin Makarantar Dalibai A Kasashen Waje,

Gwamnatin Najeriya Ta Kashe Biliyoyin Daloli Wajen Biyan Kudin Makarantar Dalibai A Kasashen Waje,

 

Bayanan babban bankin Najeriya na nuni da cewa an kashe sama da Naira biliyan Uku da rabi kan harkokin ilimi a kasashen ketare tun daga shekarar 2015 da gwamnatin Muhammadu Buhari ta hau kan karagar mulki zuwa wannan shekara da muke ciki ta 2022,

Washington DC bayan wannan kudade da gwamnatin ta kashe su kansu yan kasar sun kashe biliyoyin daloli wajen biyan kudin makaranta a kasashen waje ba tare da samun ribar wannan kudi ba na zahiri a cikin gida ba,

 

 

Irin wannan kudi dai da yan Najeriya ke kashewa a kasashen wajen na kara karya darajar Naira akan kudin dala inji masana tattalin arziki wadanda suka ce kasar na fama da karancin dalar Amurka a asusunta na ketare,

Bayan wannan kuma yawaitar yajin aikin malaman jami’o’i da na kwalejojin kimiyya da fasaha a kasar sun taimaka wajen sanya iyaye da dalibai kwadayin zuwa kasashen waje domin kammala karatun su na gaba da sakandare,

A kwanan nan ne dai kungiyar malaman jami’o’in kasar suma janye yajin aikin da suka shafe watanni fiye da 8 suna yi tare da neman gwamnati ta karawa makarantun kasar kudaden gudanarwa tare da samar da kayan aiki da kuma inganta rayuwar malamai da dalibai,

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button