LABARAI/NEWS

“Gwamnatin Nigeria ta dauko sojojin Amurka don suzo Nigeria su yiwa sojojin mu training saboda a shawo kan matsalar tsaron Nigeria”

BA’A NAN MATSALAR TAKE BA

“Gwamnatin Nigeria ta dauko sojojin Amurka don suzo Nigeria su yiwa sojojin mu training saboda a shawo kan matsalar tsaron Nigeria”

Amurka tana daga cikin manyan kasashe a duniya da take da karfin soji da kuma manyan makamai masu linzami. Ita Amurka wata kasa ce ta dauko ta don tayi training sojojin ta? Kuma abin da Gwamnatin Nigeria bata sani ba shine; kasar Amurka tana da wayo, ba zata taba turo Gwarazan sojojin ta Nigeria da Nufin bada training ba, sai dai ta tura wanda basu gama kwarewa ba. duk da Nasan cewa sojojin Amurka sun fi Na Nigeria Nesa ba kusa ba.

Sai dai Inaso ku sani; A yau a Nigeria kusan dukkan wasu makamai da Amurka take take anfani dasu wajan tunkarar abokan gaba Nigeria tana da kwatan-kwacin sa, kenan matsalar ba a wajan sojojin Nigeria yake ba, domin daga Amurka ake siyo wasu kayan Yakin. Amma Ina ne matsalar take? Shin sojojin mu ba zasu iya anfani da makaman Yakin bane? Kodai ba’a san inda ‘yan ta’adda suke ba? Tun asali abin ba’a saka gaskiya bane shiyasa haryanzu aka kasa shawo kan lamarin.

Abu daya ne Gwamnatin Nigeria tayi idan ma zai yiwu shine; a dauko hayan sojojin Amurka su Yaki ‘yan ta’adda a Nigeria shine kawai nake da Yakinin cewa karshen su Bello Turji da masu daukan nauyin su Yazo.

Wannan training da ake yiwa sojojin Nigeria bazai taba musu anfanin komai ba indai wajan yakar ‘yan ta’adda ne. domin training din zai fara aiki ne sanda aka bada umurni, su masu bada umurnin suna yiwa ‘yan ta’adda aiki bakin su daya, a cikin sojojin Nigeria akwai masu turawa ‘yan ta’adda su Bello Turji bayanan sirri.

Indai Gwamnatin Nigeria ba zata tunbuke wadannan mutanen da suka hana ruwa gudu ba, to Rasha da Ukrainian za a tura sojojin Nigeria su koyo training ba zasu iya kawo karshen ta’addanci a Nigeria ba.

Allah ya kawo mana zaman lafiya Alfarmar wannan wata Na Ramadan Amin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button