ylliX - Online Advertising Network Gwamnatin Tarayya Ta Ba Da Umurnin Sake Buɗe Kamfanin Simintin Dangote Na Obajana - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Gwamnatin Tarayya Ta Ba Da Umurnin Sake Buɗe Kamfanin Simintin Dangote Na Obajana

Gwamnatin Tarayya Ta Ba Da Umurnin Sake Buɗe Kamfanin Simintin Dangote Na Obajana

Gwamnatin Tarayya ta bayar da umurnin sake bude kamfanin simintin Dangote na Obajana da ke jihar Kogi.

Hakan ya fito yayin taron majalisar tsaro da Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta yau a fadarsa a Abuja.

Ministan harkokin ‘yan sanda, Mohammed Dingyadi da takwaransa na harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola wadanda suka kasance a taron, sun shaida wa mana labarai cewa an cimma yarjejeniya tsakanin gwamnatin Kogi da kuma kamfanin Dangote.

Aregbesola ya bayyana cewa bangarorin biyu sun amince na sake bude kamfanin simintin na Obajana, inda aka bukaci dukkansu da su mutunta yarjejeniyar.

Ministan ya kuma kara da cewa majalisar ta amince cewa za a warware dukkan batutuwa da suka janyo sabani tsakanin bangarorin saboda a cewarsa gwamnati na da zummar samarwa mutane aikin yi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button