ylliX - Online Advertising Network HAƘƘIN MIJI A KAN MATA DA HAƘƘIN MATA A KAN MIJI - AMINCI HAUSA TV
Girki Adon UwargidaFadakarwa

HAƘƘIN MIJI A KAN MATA DA HAƘƘIN MATA A KAN MIJI

HAƘƘIN MIJI A KAN MATA DA HAƘƘIN MATA A KAN MIJI

An kasa haƙƙoƙin ma’aurata zuwa kashi uku, na ɗaya haƙƙin miji a kan mata, na biyu haƙƙin mata a kan miji, na uku haƙƙin tarayya tsakanin ma’aurata.

(3) Haƙƙoƙin tarayya tsakanin ma’aurata;

1. Nuna wa juna ƙauna da soyayya;
2. Tarayya da juna cikin abin da ya sami ɗayan ko na farin ciki ko na baƙin ciki;.
3. Kowa ya dinga yi wa abokin zaman sa kwalliya da tsafta;
4. Kowa tsakanin ma’aurata ya zama mai kishin ɗan’uwansa;
5. A sami amincewar juna;
6. Kowa ya ba wa kowa daga cikin haƙƙin jin daɗi da juna ta hanyar da shari’a ta amince;
7. Kyakkyawar zamantakewa tsakanin juna;
8. Haƙuri da juna;
9. Amincewa juna;
10. Farantawa juna rai;
11. Su zama kamar abokan juna da yin shawara da juna;
12. Nuna wa juna ƙauna daga ɓangaren kowa daga cikin su;
13. Girmama iyaye da ƴan’uwa juna;
14. Taimakon juna a lokacin da wani daga ciki ya gamu da jarrabawa;
15. Wani su dinga tona asirin juna a waje;
16. Ban da cin amanar juna;
17. Ka da su dinga bayyana wani mu’amalar su ta auratayya;
18. Akwai gado a tsakanin su idan ɗaya daga cikinsu ya fara rasuwa;

Wannan saƙo ne ga dukkan ma’aurata su zama su yi nazarin wannan saƙo kowa ya ga abin da yake yi a ciki, domin mu gudu tare mu tsira tare. Allah ya ba mu ikon kiyaye haƙƙin juna. Ya cika zukatanmu da ƙauna da soyayya da girmamawa tsakanin mu da iyalinmu. Sirrin ma’aurata da zai sa aure ya wuce yadda ake tunanu, wasu masana sun bayyanar da wasu abubuwa da ke da matuƙar muhimmanci ga sababbin ma’aurata. Idan kuwa har ma’aurata za su ɗauki waɗannan abubuwan da kuma aiwatar da su, to ba shakka auren su zai zama mutu ka raba.

Yana da matuƙar muhimmanci ga amarya da ango da suka yi aure ba da daɗewa ba, su ware wasu watanni don angwanci, “Honeymoon” a Turance, a waje ɗaya, da bayyanar ma juna wasu abubuwa da ya kamata kowa ya kiyaye. Haka ma akwai buƙatar ango da amarya su nisanta kan su na ƴan wasu kwanaki, ko dai ango ya yi tafiya ko amarya ta yi tafiya, wanda hakan zai sa a yi marmarin juna. Idan rai ya ɓaci a nisanci juna. Kamar yadda ya zo a Hadisin Sayyidina Aliyu, lokacin da suka sami saɓani da Nana Faɗimah R. A., sai ya koma masallaci, har ya huce, nisantar juna a lokacin fushi, yana haka yanke hukuncin da za a yi nadama.

Akwai buƙatar ma’aurata su fahimci cewar aure kamar sabon aiki ne, don haka kowa a tsakani ya riƙe aikin shi ƙwarai da muhimmanci, ka da ya samu matsala da shugabanshi a wajen aiki daga samun sabon aiki. Haka babu wani tsafi ko suddabaru da zai sa a ce an san halin juna ɗari bisa ɗari, don haka sai an dinga taka tsantsan wajen kyautata ma juna. Babu dalilin da zai sa a ba za a zama abokan juna ba, ka da wani abu na ɓoyo ya shiga tsakani, akwai buƙatar bayyanar da komai ga juna, ba tare da wasu ƴan bayan fage na ba da shawarar yadda za ku magance matsalar ku ba. Hakan na na aure ya wuce yadda ba a taɓa tsammani ba.

Allah ya sa mana albarka a dukkan rayuwarmu ta aure. ALHAMDULILLAH
النساء اهل الجنة ✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button