Girki Adon Uwargida

Hanyoyi 6 Da Masoya Zasu Iya Daidai Kansu A Lokacin Sabani

Hanyoyi 6 Da Masoya Zasu Iya Daidai Kansu A Lokacin Sabani:

SHARE 💞

Aminci Hausa TV

Babu soyayyar da ba a samun matsala a cikinta. Kamar yadda babu zaman auren da babu matsala.

Sai dai ba ko yaushe bane ya dace mutane musamman masoya su rika jawo mutane cikin matsalolinsu ba. Dole ne su koyi yadda zasu rika warware duk wasu rashin fahimta daya taso musu.

Related Articles

Ga wasu matakan da masoya zasu iya dauka a junansu a lokacinda suka samu sabani.

1: Daukan Mataki- da zaran matsala ta kunno kai a tsakanin masoya su hanzarta su magance abun kada su ce zasu bari sai wani lokacin hakan kesa karamar matsala ta girma ta dawo babba.

2: Sauraran Juna- a wajen zaman tattaunawa kada kowa ya dauka shine mai gaskiya don haka shi za a saurara.
Kowa yayi hakurin sauraran kowa domin fahimtar juna da kuma gano ta inda aka samu matsalar domin gyara.

3: Tashin Tashina-idan ana zaman sulhu ba a so ana yawan dawo da abunda ya wuce. Abunda ya jawo matsalar a yanzu nan ya kamata a maida hankali amma ba tone tone ba.

4: Kiyaye Kalamai- ya zama wajebi wajen zaman sulhu masoya su san irin kalaman da zasu yi amfani dasu wajen maida bayani.

Musamman wanda yake ganin shi aka yiwa laifi ya guji furta kalaman da zasu iya tunzura gudan.

5: Fadin Gaskiya- kada masoya su yiwa juna nuku-nuku a wajen maida magana. Kowa ya fadi gaskiyar abunda yake damunsa domin a kawo karshen matsalar saboda gaba.

6: Ku Yafe- kada ku tashi a wajen wannan sulhun sai har kun gamsar da junanku abunda ya faru ya wuce kuma da alkawarin ba za a sake samun hakan ba.

Da fatan masoya zasu kula kuma suyi amfani da wannan shawaran.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button