LABARAI/NEWS

HANYOYIN DAINA MASTUBATION DA ILLOLINTA

HANYOYIN DAINA MASTUBATION DA ILLOLINTA

 1. Kaucewa kallon finafinan batsa
 2. Dena kallon hoton da tsiraici yai yawa ko ya bayyana a ciki, ballantana kuma hoton tsiraicin
 3. Dena zama kai kadai akoda yaushe. Ka koyi zama cikin jama’a koda bakaso, ko zama a masallaci
 4. Kauracewa mu’amala da Mace wacce ba muharramarka ba, kai koda muharramarka ce yanzu abubuwan sun baci inkanajin bazaka iya rike kanka ba… kai nesa da magana da ita.
 5. Kauracewa zancen batsa yayin waya da wata ko wani.
 6. Rage yawan tunanin Mace ga Maza ko tunanin Namiji ga Mace muddin hakan na haifar da matsala
 7. Tuba ga Allah tare da daukar Alkawarin rashin sake aikatawa har abada.
 8. Bijirewa dukkan wani nau’in abu mai tayar Maka da sha’awa. Tare da tuna cewa gwargwadon tsananin son kai sa6o inka kaurace masa gwargwadon kimarka agun Allah kenan
 9. Rage yawan dakon finafinai a waya ko kallonsu a TV
 10. Jajircewa koda kaji idan baka yi shiba kamar zaka mutu ka daure karka aikata shi. Nemi lemon tsami ka jiqa kasha awasu sukan samu hakan ya karya musu sha’awa amma ba duk ba..
 11. Jajircewa ga azumin Nafila musamman bin ayarin azumin Litinin da Alhamis.
 12. Kaucewa karanta Novels da littattafai na batsa.

WADANNAN SUNE HANYOYIN BI DOMIN KAURACEWA DABI’AR AUREN SABULU

Idan kasan me ake kira fyade… toh masturbation yiwa kai da kai fyade ne, cin zarafin kai ne (self rape)

Babu kyau! Shine dalilin faduwar Maza da yawa ayau, Mutum yai aure ya doshi iyali kafin ma yakai ga Macen ko seconds 30 yace yai releasing, this is so embarassing, Amaryarka ta gama gyara jiki ankawota ashe kai din sorry ne ka kashe kanka tunda kuruciya.

Kema ki dena tun kafin kima kanki illar da zaki hadu da massive PID infection tubes dinki su toshe samun ciki ya gagareki.

Bazaku ta6a hada wannan aiki da jima’i ba, jikinku yasan ba jima’i bane, kuma daban zai reacting. Don haka gara anemi sana’a ai aure samari.

Mantuwa, yawan wasi-wasi, Raunin azzakari, cudewar tunani, karancin sha’awa, rage karfin gani, yoyon fitsari, da ciwon mafitsara (UTI), duk na daga illolin da auren sabulu ka iya yiwa mutum.

Ai hattara zai iya muku illar dundun-dun wato permanent, ta yadda wataran sam gaban naka ma zaike rauni wajen mikewa komi zakai kuwa. Sannan zaka je limit da ko kai aure zakaji inba masturbation kai ba bakajin daidai.

In andena kuma azamo active motsa jiki sosai, domin boosting din tsokokinka domin hakan yai boosting sinadarin testosterone dinka ya zamto kai maintaining na mazantakarka, Ai kokari komi tsanani kai tuban gaske domin in dopamine ya fara fita denawa sai anyi da gaske addict ake zama, dage kaci me kyau, kake samun isashshen bacci. A kuma qara da addu’a, in ansami hali ai aure shine magani kankat

KAI AKARSHE MA DE KA TUNA HARAMUN NE FA ADDINI YA HANA

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button