ylliX - Online Advertising Network Har Yanzu Katsina Ba Ta Yafe Wa Ɗan Bindiga Ado Aliero Ba, Gwamna Masari - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Har Yanzu Katsina Ba Ta Yafe Wa Ɗan Bindiga Ado Aliero Ba, Gwamna Masari

Har Yanzu Katsina Ba Ta Yafe Wa Ɗan Bindiga Ado Aliero Ba, Gwamna Masari

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari, ya ce har yanzu gwamnatin Katsina ba ta yafe wa Ado Aliero ba, ɗan bindigar da take nema ruwa a jallo duk da naɗin sarautar da aka yi masa a Zamfara

Gwamnan Jihar Aminu Bello Masari ne ya shaida wa Majiyar Focus News Hausa, BBC cewar sun yi mamakin jin nadin sarautar da aka yi masa, sai dai ya ce ko da a ce Ado Aliero ya dena ayyukan ta’adanci a Zamfara har yanzu a wajen su bai daina ba

Ya bayyana cewa tun bayan faruwar wannan lamari, ya yi ƙoƙarin tuntuɓar Gwamnan Zamfara Bello Matawalle, amma bai same shi ba domin tattauna wannan batu

Gwamna Masari ya ce har yanzu gwamnatin Katsina na kan bakarta ta neman Ado Aliero ruwa a jallo bisa zargin kashe mutanen Kadisau da kashe mutanen Faskari

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button