Harin da Boko haram ta kai Rundunar Sojojin Najeriya Sun Sha Al’washin Fitowa Da Sabbin Dabarun Magance Matsalolin Tsaron

Harin da Boko haram ta kai Rundunonin Sojojin Najeriya Sun Sha Al’washin Fitowa Da Wasu Sabbin Dabarun Magance Matsalolin Tsaron Da Ke Addabar Kasar
Majalisar tsaron Najeriya ta ce ta yarda kasar na cikin mawuyacin hali inda matsalolin rashin tsaro ya ke cigaba da addabar al’umma
Wannan dai na daga cikin abububwan da aka tattauna yayin taron majalisar koli ta harkokin tsaron Kasar da aka yi ranar Alhamis karkashin jagorancin Shugaba Muhammad Buhari
Wannan dai na zuwa yayin da lamarin tsaro ke kara tabarbarewa a kasar da har ta kai yan majalisar dattawa daga bangaren adawa kiran da a tsige shugaban kasar
Da yake wa manema labarai bayani bayan kammala wannan taron mai bai wa shugaban kasar shawara kan harkokin tsaro Manjo-janar Babagana Munguno mai ritaya ya ce majalisar ta amsa cewar kasar na cikin mawuyacin hali
Kuma shugaba Muhammad Buhari ya fahimci irin damuwar da yan kasar ke ciki game da hakan