LABARAI/NEWS

Harin Gidan Yarin Kuje: An Nemi Abba Kyari Da Wasu Tsoffin Gwamnoni Biyu An Rasa

Harin Gidan Yarin Kuje: An Nemi Abba Kyari Da Wasu Tsoffin Gwamnoni Biyu An Rasa

Rahotanni daga babban birnin tarayya Abuja sun bayyana cewa an nemi tsohon Mataimakin Kwamishinan ‘Yan sanda DCP Abba Kyari da Tsofaffin gwamnonin Taraba da Plateau Joshua Dariye da Jolly Nyame an rasa, bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari a babban gidan gyaran hali na Kuje, dake babban birnin tarayya Abuja.

A daren jiya ne dai da misalin karfe 10 na dare aka Kai hari gidan yarin, inda aka jiyo fashewar abubuwan fashewa a yayin harin.

Abba Kyari, wanda yake fuskantar tuhuma tare da wasu abokan aikin sa guda biyu suna zaune a gidan yarin tun bayan da kotu ta tura su.

Tsohon gwamnan jihar Taraba, Joshua Dariye da takwaransa na Plateau, Jolly Nyame, waɗanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yafe wa har yanzu basu fita daga cikin gidan yarin ba, duk da yafiyar da akayi musu.

Sai dai Kamar yadda jaridar “the Nation” ta ruwaito, babu tabbas ko bacewa sukayi ko Kuma an kwashe su ne domin kula da lafiyar su.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button