LABARAI/NEWS

HARKALLAR HODAR IBILIS: yanda hukumar NDLEA ta dana ma Dan Sanda DCP Abba Kyari Tarko ya fada kuma ta kama shi Dumu Dumu

HARKALLAR HODAR IBILIS: yanda hukumar NDLEA ta dana ma Dan Sanda DCP Abba Kyari Tarko ya fada kuma ta kama shi Dumu Dum

HARKALLAR HODAR IBILIS: yanda hukumar NDLEA ta dana ma Dan Sanda DCP Abba Kyari Tarko ya fada kuma ta kama shi Dumu Dumu .
___________

Hukumar hana sha da kuma fataucin miyagun kwayoyi a Nijeriya NDLEA tace yanzu haka Abba Kyari da abokan harkallar sa na hannun su

Hukumar NDLEA
Hukumar NDLEA ta bayyana cewa DCP Abba Kyari da abokan harkallar sa da ake zargi da hannu dumu-dumu a safara da harƙallar hodar ibilis na tsare a hannun hukumar.

Kakakin hukumar Femi Babafemi ya bayyana cewa mutum biyar ɗin da ake zargi duk suna tsare a hukumar.

Ya kara da cewa hukumar za ta yi bincike mai zurfi akai kuma zata sanar da duniya abinda ta gano kai tsaye.

Ƴan sanda sun damka Abba Kyari ga Hukunar NDLEA

Kakakin rundunar ƴan sandan Najeriya Muyiwa Adejobi ya bayyana cewa rundunar ta damke wasu jami’an ƴan sanda dake aiki karkashin rundunar tsaro ta musamman IRT da ake zargi da hannu a badaƙalar harkallar hodar ibilis a kasar nan.

Cikin waɗanda aka damke harda fitaccen ɗan sanda DCP Abba Kyari da ake zargin sa da hannu dumu-dumu a harƙallar hodar Ibilis da wasu jami’ai huɗu.

Sakamakon binciken ƴan sanda ya nuna cewa ciki harda haɗin bakin wasu jami’an hukumar NDLEA wanda da su masu safarar ke hada baki a tashar jirgin saman Enugu ba tun yanzu ba.

Muyiwa Adejobi ya kara da cewa sufeto janar din ƴan sanda ya umarci da a miƙa su duka hukumar NDLEA domin a ci gaba da bincike akai sannan a hukunta su.

Wadanda aka kama sun haɗa da DCP Abba Kyari, ACP Sunday Ubuah, ASP James Bawa, ASP John Umoru wanda ya gudu, sai kuma Insp. Simon Agrigba da John Nuhu.

Harkallar Hodar Ibilis

A wata sabuwar harkallar da safarar muggan kwayoyi da hukumar NDLEA ta bankaɗo an sami babban ɗan sanda Abba Kyari da hannu dumu-dumu cikin jigila da kasuwancin su tun daga Najeriya har kasar Brazil.

Idan ba a manta ba Kyari na cukuikuye har yanzu cikin badaƙalar cin hanci, almundahana, zamba da yaudara wanda rikakken dan damfara Hushpuppi ya fallasa shi

Sai dai kuma a wancan lokaci Kyari ya musanta hannu da ya ke da shi a harkallar, yana mai cewa ɗinkin jamfa ne ya haɗa shi da Hushpuppi ba abinda aka zarge shi da shi ba.

A doguwar takardar da hukumar NDLEA ta fitar ranar Litinin, hukumar ta bayyana ta ce ta gano ashe Abba Kyari ƙasurgumin mai safarar muggan kwayoyi ne sannan ashe yana daga cikin gaggan ƴan kungiyoyin masu safara da harƙallar muggan kwayoyi na duniya daga Brazil-Ethiopia-Najeria.

A wurin taron manema labarai da hukumar ta yi a Abuja hukumar ta ce:

” Abba Kyari da kanshi ya nemi wani jami’in hukumar NDLEA din domin su tattauna wani muhimmin magana kamar yadda ya shaida masa a waya. Bayan sun haɗu bayan sallar juma’a a wannan rana. Sai Abba Kyari ya fara bayanin cewa jami’an sa sun kama wani kasurgumin mai sfara munggan kwayoyi a Enugu. Amma abinda ya ke so shine zai damka wannan mutum ga hukumar NDLEA, amma kuma yana son maimakon a baiwa hukumar tarin hodar ibilis din da aka kama shi da su, yana so ne a raba. Ya dibi wani abu ya bai wa hukumar wani abu.

” Da jami’in mu ya sanar da hukumar abinda ake ciki sai muka ce ya ci gaba da tattaunawa da Abba Kyari har sai an kai karshe.

Hukumar ta ce daga nan sai Abba Kyari ya rika ganawa da wannan jami’i amma kuma bai sani cewa duk abinda suke yi ana ɗauka ba saboda yadda da yayi da jami’in

” Abba Kyari har kuri ya ke cewa yana kula da jami’an sa babu matsala ta ɓangaren sa. Yanzu dai za a raba hodar ibilis din gida biyu, zai ɗauki rabi ya kawo hodar ƙarya a saka ya cike wanda aka ɗiba. Kilogiram 15 da ya ɗiba an raba wa waɗanda suka fallasa harƙallar, da jami’an da suka yi aikin cafke mai safarar.

” Bayan haka sai Kyari ya nemi ya aiko da kuɗin da zai biya na hodar amma kuma jami’in NDLEA ɗin ya ce lallai sai dai su haɗu ido na ganin ido. Da Kyari yazo sai suka shiga cikin mota amma kuma motar duk an sassaka mata na’urar ɗaukan hoto, bidiyo da murya.

Hukumar ta ce ta nemi Kyari ya bayyana a gabanta domin ya kare kansa amma ya ki, shi ne ya sa hukumar ta bayyana shi ‘WANTED’. Kuma jami’an Yan sanda suka kamo shi.

Shi dai Abba Kyari Allah ya masa baiwa ta iya kama masu garkuwa da mutane da kuma masu mugun aiki a Nijeriya. Abinda yasa yayi ta fadawa rikice-rikice iri da kala.

Sai dai wani mai Sharhi kan lamuran da suka shafi ayyuka masu Sarkakiyya yace akwai yuyuwar a shi Dan sanda DCP Abba Kyari na kokarin gano wasu abubuwa cikin jama’an ta hukumar NDLEA. Yayi amfani da basiran aiki domin gano inda harkallar take samun daurin Gindi.
Su kuma jami’an hukumar sukayi amfani da tasu basiran suka afka da shi cikin komar su.

Ko dai yaya ne Abba Kyari yana da cikakkiyar damar kare kansa domin fita cikin zargin. Duda cewa akwai faifayin bidiyo da hukumar ta nada Amma bincike ne kawai zai fayyace mai Gaskiya cikin lamarin a halin yanzu.

Ko yaya kuke kallon lamarin na Abba Kyari a halin yanzu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button