Islamic Chemist

Harkar maganin gargajiya a cikin al’ummar Hausawa

  1. Harkar maganin gargajiya a cikin al’ummar Hausawa
  2. Harkar maganin gargajiya a cikin al’ummar Hausawa ba sabuwar harka ba ce. Tsohuwa ce kuma a yanzun ta haɓaka ta bunƙasa ta zamo business mai zaman kansa. Fara tun daga kan ƴan magori irin na da can da wanzamai da ƴar me ganye zuwa masu maganin gargajiya na zamani waɗanda ba sa jin kunya ko tsoron kiran kansu da laƙabin (dakta), wanda sannu a hankali wasa da sakaci wajen kiran mutane da wannan laƙabi ya yaɗu har cikin masu ruƙuya da ƴan Islamic Chemist. Abin har ya zamana cewa gane waye dakta mai MBBS, waye dakta mai PhD, wane kuma aka ba shi na girmamawa, ko kuma waye likitan dabbobi, sannan waye kuma ɗan magori da mai yin ƙaho abu ne mai wuya. Mun zama al’ummar ‘kowa dakta’.

 

Yaɗuwar wannan harkar ta maganin gargajiya ba ta tsaya a Nigeria ba, ta tsallaka zuwa ƙasashen maƙwabta, musamman jamhuriyar Nijar. Tare da cewa a Nijar ɗin suna da nasu masu maganin gargajiyar, amma namu sun zama ‘international’. Suna tsallaka su ci kasuwanni a Maraɗi da Ƙwanni da Diffa da Dosso da ma Niamey. A garin haka sun koya wa masu maganin gargajiyar Nijar irin ƴan dabarun su da sakin baki da aka san su da shi. Kana tafe a bakin kasuwa ko gefen masallaci sai ka jiyo lasifika na ruri. Ana ta lissafin cututtukan da za ka iya cewa they are peculiar to Hausawa; basir, sanyi, ƙarfin maza da sauransu. Ka ji ana ta rantse-rantse don nuna sahihancin maganin da kuma nuna cewa ba wani magani kamar shi.

A yawan tambaye-tambaye na sai da na tambayi cewa wai ba wata doka ce a nan jamhuriyar Nijar da ke kula da irin wannan salon kasuwanci? Aka amsa min da cewa ba ruwan iko da su. Sai na tuna maganar mawaƙi da yake cewa: “Nigeria da Nijar daidai suke”.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button