ylliX - Online Advertising Network Hatsarin Mota ya ritsa da 'Yan maulidi a Jihar Neja mutum Uku Sun mutu. - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Hatsarin Mota ya ritsa da ‘Yan maulidi a Jihar Neja mutum Uku Sun mutu.

Hatsarin Mota ya ritsa da ‘Yan maulidi a Jihar Neja mutum Uku Sun mutu.

A jiya Asabar ne, aka gudanar da Maulidin Annabi Muhammad (S.A.W.) a Garin ( Kuta ) Karamar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja, “inda aka rasa rayuka aƙalla mutum Uku, wasu adadi kuma Sun Samu raunuka.

Al’umma a Garin Minna Sun tsunduma cikin Jimami Saboda Rasa rayukan Waɗannan samari a yayin dawowarsu Halartan Maulidi a Garin Kuta dskeo ƙaramar Hukumar shiroro a Jihar Neja.

Lamarin Ya Faru ne a Hanyar dawowa Daga wurin Maulidin Annabi Muhammad (S.A.W.) da akayi a garin na kuta inda Matasa da dattijai mata da yara suka halarci taron don Nuna farin ciki da haihuwan fitayyen Halitta (S.W.A.).

To Ammah dai wani Zargi da Jama’a keyi akan Faruwan Lamarin, Ana zargin rasa rayukan na Matasan ya biyo bayan Tukin wuce ka’ida da guje-gujen dasu Marigayan sukeyi kafin afkuwar Lamarin kamar yadda dama kusan Duk shekara sai irin hakan ya faru na rasa rayuka ko Samun Rauni Yayin dawowa daga wurin Wannan Maulidin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button