HATTARA DAI JAMA’A: Barayin Waya Sun Fito Da Sabuwar Hanyar Satar Waya Yan Uwa Mu Kula:-

HATTARA DAI JAMA’A: Barayin Waya Sun Fito Da Sabuwar Hanyar Satar Waya Yan Uwa Mu Kula:-
A Daren Jiya Barayin Waya Sukai Amfani Da Wannan Makatar Da Suka Hada Da Kuke Gani Mai Dauke Da Sanda Da Jan Kyalle Da Kusa A Jiki Suka Sace Ma Mahaifi Na Waya.
Daga Usman Kwankwaso
Mahaifina Yace Min Ya Gama Taqara Wajan Karfe 1 Na Dare Ya Kwanta Sai Yasa Chaji, Koda Ya Tashi Da Asu Ba Sai Yaga Sai Chaja Da Wannan Itacen, Sun Yi Amfani Da Shi Sun Sace Wayar Ta Window, Yadda Kuwa Suke-yi Shi ne Sandan Suke Zurawa Su Dakko Chajan Tunda Tana Chaji Kuma Chajan Ba Fita Zai A Jikin Wayan Ba, Yayin Da Suka Dakko Wayan Sai Su Gudu.
Da Garin Allah Ya Waye Sai Aka Sanar Da Wani Bawan Allah Mai Suna Abubakar Ahmad Yana Gyaran Waya ne, Shi Kuma Ya Sanarwa Abokanan Aikin Sa, Cikin Ikon Allah Dai Wayar Nan Yanzu Haka Tana Hannun Mahaifi Na Amma Banu Simcard, Amma Fa Wayan Anyi Transactions Yakai 4, Kuma Na Karshen Da Aka Kama An Tafi Da Shi Dan Cigaba Da Binciki.
Nayi wannan Maganar Ne Saboda Yan Uwa Matasa Da Wanda Suka San Suna sanya Chaji In Zasu Kwanta Da Su Dunga Boye Wayar Su, Imam Chajin Ba Dole Bane Ba A Hakura Da Shi, In Ba Haka Ba Kana ji Kana Gani Wani Barawon Zai Rabaka Da Wayar Ka, Kuma Ya Goge Maka Record Din Dake Ciki, Allah Ya Kara Tsare Mu.