Videos

Honeymood din maishadda da Hassana Muhammad ya canza salo

Honeymood din maishadda da Hassana Muhammad ya canza salo

Tun bayan da wa’yannan yan kannywood din biyu sukayi aure shikkenan idon mutane ya hau kansu wanda bayan wannan bikin nasune aka hangesu achan kasar Dubai domin yawon cin amarci acan wanda hakan ba karamin jawo hankalin mutane yayi ba akansu dokin daman ansa Bashir maishadda yana da kudi a hannunsa

Sai dai kuma yayin wannan hutun nasu sun jawo magana wanda wasu ke ganin sam wannan abubuwan basu dace dasuba saboda su yanzu ba kamar sauran jarumai bane sun shiga sahun manyan mutane tunda darajar su da sagu daga marassa aure zuwa masu aure

Sai dai kuma ta wani bangaren abin nasu yayi matukar nawa mutane sha’awa saboda kowanne rai yanason hutu da kuma kasancewa cike nishadi da kuma farin ciki an yabawa maishadda bisa wannan nauyin hutun nasu daya dauka

Yanzu prodecer Bashir maishadda yabar mutane sai surutai suke tunda daman kowa yasan akwai wa’yanda abin magana baya musu wuta koya sukaga abu sai sun tofa wani abu akai shi yasa yayi biris ya rabu dasu

Daga ƙasar Dubai yayin hutun jaruman sai kuma aka hangi fuskokinsu acan kasa mai tsarki wato kasar Saudi Arabia sunje umara da kuma ziyarar shugabanmu Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallam

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button