FadakarwaLABARAI/NEWS

Hoton matashi mai bindi tsawon 70cm ya bazu,ana cewa Yesu ne aka sake haihuwa

Hoton matashi mai bindi tsawon 70cm ya bazu,ana cewa Yesu ne aka sake haihuwa

Deshant Adhikari mai shekaru 16 ya zama abin sha’awa a duniyar intanet bayan da ya kasance yanada wata baiwar halitta da ba kowa ke da ita ba ,ya kasance an haifeshi da wutsiyar gashi kamar bindi,wanda tsayin sa yakai mita 70.

Iyayen Deshant sun so su gutsire gashin

Iyayen sa su farga da wannan bakon lamari ne bayan kwanaki 5 da haihuwar sa, Mirror.co.uk ta ruwaito cewa iyayensa su tashi hankulansu inda suka kasa zaune suka fara ziyartar asibitoci na gida da waje don ganin kawai an cire wannan gashi.
Hankalin su bai kwanta ba har sai da wani limamin yankin ya fayyace musu cewa Deshant Adhikari ya kasance wani daga cikin Allolin su ne ya sake dawo wa duniya. Limamin ya kara da cewa Deshant wani gunkin Hindu daya fito daga tsatson Birai wanda aka fi sani da Lord Hanuman, wanda ya zo a tarihin Hindu. Wani Mai shirya fina-finai Puskar Nepal wanda ya samu damar zantawa da Deshant ya ce limamin ya umurci iyayen yaron da kada su kuskura su yanke ko su tsefe gashin saboda saboda akwai wasu sirrika a tattare da gashin.

Deshant ya ce da farko abin kunya yake bashi

Yaron ya bayyana cewa da farko abin kunya yake bashi amma yanzu yariga ya saba kuma ya daina boyewa zai fito da shi ya nunawa duniya.
Bidiyo na ya yadu a kafar zumunta na Tik Tok inda acyanzu mutane da yawa suke min lakabi da yaro mai wutsiyar gashi,inajin dadi game da hakan”.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button