Hotuna kafin aure na kara yaduwa ta kowacce irin siga amarya da angon na daƙuwa ko ka ga sun rungumi juna

Hotuna kafin aure na kara yaduwa ta kowacce irin siga amarya da angon na daƙuwa ko ka ga sun rungumi juna
ko ka ga ya damƙo ƙugunta ko an yi sumba to alama ce da ta ke nuna cewa iyayen banza ne su ka raini ma’auratan ko kuma ma’auratan sun bijirewa tarbiyyar da a ka ba su ne ko kuma dama can sun saba damƙar juna tun kafin auren
Hakanan in ka ga ballagazar amarya ta na ta cashewa a wajen bikinta ko ka ga mazarin ango ya na ta botsare-botsare cikin rawa da sunan murna
to dukansu ba su da tarbiyya kuma su ɗin hoto ne mai magana na irin gurɓatattun ƴaƴan da za su zazzago duniya ne Sun cuci ƴaƴansu, kuma sun cuci al’umma da suke shirin haifo baragurbi
Kwata-kwata babu cinyewa a fitsara lokacin biki Angwaye da amaren da suka haifo manyan malamai da attajirai masu dattaku tabbas ba su yi fitsara irin wannan ba