HOTUNAN Shugaban Boko Haram na yanzu Bakoura wanda ya karbi mulki daga hannun Shekau Abubakar

HOTUNAN Shugaban Boko Haram na yanzu Bakoura wanda ya karbi mulki daga hannun Shekau Abubakar
Bakoura Buduma shugaban kungiyar Boko Haram na yanzu sun bayyana a yanar gizo a yayin da ake ci gaba da gwabza fada tsakanin ‘yan kungiyar masu jihadi da ake kira ISWAP da Boko Haram a dajin Sambisa
Bakoura Buduma wanda aka fi sani da Bakoura Doro ko kuma Abou Oumaymah ya zama shugaban kungiyar Boko Haram bayan mutuwar Abubakar Shekau
Bakoura wanda ya karbi ragamar shugabancin kungiyar ta Boko Haram shi ne ke jagorantar kazamin fadan da ake yi da kungiyar ISWAP a yankin yammacin Afirka a cikin ‘yan watannin da suka gabata a cewar wani kwararre kan yaki da ‘yan ta’addan
Idan dai za a iya tunawa kungiyar Boko Haram da kungiyar ISWAP a yan kunar yammacin Afirka na fama da rigingimun da ba a warware su ba wanda ya kawo kashe mayakan Jihadi da dama a cikin kungiyoyin
An kuma kashe Shakau Abubakar bayan wani harin bazata da kungiyar ISWAP ta kai a yankin yammacin Afirka (ISWAP) a sansanonin Boko Haram da ke kusa da tafkin Chadi a arewa maso gabashin Najeriya