Hukumar DSS Ta Gano kaya na Sojoji 24, da kudi Sama da Miliyan 100 A Gidan Mamu

Hukumar DSS Ta Gano kaya na Sojoji 24, da kudi Sama da Miliyan 100 A Gidan Mamu
Sabbin takardun kotu sun bayyana yadda hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta kwato makudan kudade sama da Dala 151,000 sama da N105,000,000 a wani samame da suka kai gidan mawallafin Desert Herald Tukur Mamu
Amma bisa ga takardun da wannan kafar yada labarai ta samu kayayyakin da aka gano a gidan Mamu sun hada da kakin sojan ruwa guda 16, kakin Sojoji 8 kudin kasashen waje daban-daban, dala 151,000 da tsabar kudi sama da Naira miliyan daya
ta tattaro maku cewa Sauran abubuwan da aka dawo dasu sun hada da kwamfutar tafi-da-gidanka 6 kwamfutar hannu, na’urorin sadarwar dabara daban-daban da kuma na’urar daukar hot Sai dai dangin Mamu sun ce kayan sojoji na ‘yan uwan Mamu ne
Malamin addinin musuluncin nan Ahmed Gumi ya bukaci hukumar ‘yan sandan sirri da ta saki Mamu ko kuma ta gurfanar da shi a gaban kotu cikin gaggawa, Kamar yadda Wakilin mu ya bibiya lamarin bisani ya kawo maku wannan dambawar da ake Yi